'Yan ci ranin Sudan 13 sun mutu bayan kifewar kwale-kwalensu
February 9, 2024'Yan ci ranin Sudan 13 ne suka mutu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a gabar ruwan Tunisiya yayin da wasu 27 suka yi batan dabo, a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai ta barauniyar hanya, kamar yadda kamafanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito.
Karin bayani:Muhawara kan takaita bakin haure a Faransa
Mai magana da yawun kotun birnin Monastir Farid Ben Jha ya shaida wa kotun cewa daga cikin fasinjoji 42 da suke jirgin, biyu kacal aka tarar a raye, kuma ana ci gaba da neman sauran da suka lume a ruwa, bayan sun taso daga garin Jebiniana kusa da birnin Sfax, sakamakon kazantar yakin basasa a Sudan.
Karin bayani:An gano gawarwakin 'yan ci-rani guda biyu a cikin jirgin ruwan da ke dauke da mutane sama da 200 a Spain
Kasashen Tunisiya da Libiya sun kasance babbar hanyar da masu tsallakawa Turai ta barauniyar hanya ke bi, inda bara kadai hukumomin Tunisiyan suka samu nasarar cafke 'yan ci-rani kusan dubu saba'in da ke kokarin ketarawa.