1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

WHO na son ba ta hanyar iya kai agaji a Zirin Gaza

January 10, 2024

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bukaci Isra'ila da ta bai wa jami'anta da sauran ma'aikatan MDD dama domin ganin sun shigar da agajin jinkai a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4b5pu

Shugaban hukumar ta WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce sau shida aka yi ta soke tsare-tsaren kai kayayyaki a arewacin Gaza, tun ranar 26 ga watan jiya, saboda rashin tabbacin kare lafiyar ma'aikatan hukumar.

Ya bayyana takaicin yadda suke dauke da kayayyakin da ake bukata ba kuma tare da sun samu damar shigarwa ba, saboda tsananin hare-hare da Isra'ila ke kai wa a yankuna na Zirin Gaza.

Daga cikin matsalolin dai sun hada da rashin makamashi da katse hanyoyin sadarwa da ake yi, baya ga luguden bama-bamai da ake ta yi.

Yanzu dai asibitoci 15 ne ke aiki kuma ba na cikakken lokaci ba, sannan kuma akwai karancin ruwa da rashin tsari na tsaftar muhalli, wadanda duk ke zama matsaloli da ke bukatar dauki a Gazar.