1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fashewar tankar mai a Najeriya: Mutun kusan 100 sun mutu

January 18, 2025

Lamarin ya auku da kimanin karfe 10 na safiyar Asabar a yayin da jama'a suka yi tururruwa domin kwasar ganima a lokacin da wata tankar mai shake da lita 60,000 na fetur ta fadi a jihar Neja.

https://p.dw.com/p/4pKUk
Nigeria Öltransporter explodiert Symbolbild ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/Str

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 70 sun halaka sakamakon fashewar tankar mai a safiyar wannan Asabar a jihar Neja a magamar hanya ta Dikko da ke bisa hanyar da ke hada Abuja fadar gwamnatin kasar da birnin Kaduna.

Lamarin ya auku ne da kimanin karfe 10 na safiya a yayin da jama'a suka yi tururruwa domin kwasar ganima a lokacin da tankar man mai dauke da lita 60,000 na fetur ta tuntsire kamar yadda hukumar kiyaye hadura ta Tarayya ta shaidar.

Shugaban hukumar Kumar Tsukwam ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kawo wannan lokaci an tantance mutane 70 da suka mutu a wannan lamari da aka cika samun aukuwar irinsa a Najeriyar.

Dama dai a watan Oktoban bara hadari makamancin wannan ya rutsa da rayukan mutane akalla 170 a jihar Jigawa da ke arewacin kasar da ta fi ko wace kasar yawan al'umma a nahiyar Afirka.