1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rasa rai lokacin tada mazauna wata unguwa da ke Legas

Mohammad Nasiru Awal
April 10, 2017

Daruruwan mazauna unguwar sun tsere cikin kwale-kwale a yankin na ruwa da ke Legas lokacin da 'yan sanda suka fara kai samamen.

https://p.dw.com/p/2b0uU
Nigeria schwimmender Slum in Lagos
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Elshamy

An harbe mutum guda har lahira sannan daya ya ji rauni lokacin da 'yan sandar jihar Legas suka yi amfani da karfin hatsi wajen tada mutane sama da 2,000 mazauna wata unguwa da ke kusa da bakin ruwa, sannan sun kuma ruguza wata unguwar talakawa, inji shaidun ganin ido.

Daruruwan mazauna unguwar sun tsere cikin kwale-kwale a yankin na ruwa da ke Legas lokacin da 'yan sanda suka fara kai samame a ranar Lahadi. Wannan dai shi ne karo na hudu cikin watanni shida da ake amfani da karfi wajen tada mazauna unguwar Otodo Gbame.

Wata 'yar unguwar ta ce bayan da mutane suka tsere cikin ruwa, wani ayarin 'yan sanda da suka kai mutum 20 sun bazu cikin unguwar sun zuba kananzir kan kan dakunan katako da karfe sannan sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye da albarusai a kan mazauna da ke ihu daga cikin kwale-kwalensu.

Morayo Adebyo na kungiyar Amnesty International a Najeriya ya ce an yi ta harbi kan mazauna unguwar da suka koma don su kwashe kayansu.