1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Makomar Wagner bayan babu Prigozhin

Binta Aliyu Zurmi LMJ
August 24, 2023

Shugaban kamfanin sojojin hayar Rasha wato Wagner, Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hadarin jirgin saman 'yan kasuwa. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta kasar, ta sanar da cewa yana cikin mutane 10 da ke jirgin.

https://p.dw.com/p/4VY4w
Rasha | Rundunar sojojin haya | Wagner | Yevgeny Prigozhin | Mutuwa
Shugaban rundunar sojojin hayar Rasha ta Wagner Yevgeny PrigozhinHoto: Press service of "Concord"/REUTERS

Shugaban rundunar sojojin hayar Rashan ta Wagner Yevgeny Prigozhin dai, na da shekaru 62 a duniya. Tsohon na hannun daman Shugaba Vladmir Putin na Rashan, wanda suka raba gari bayan da shugaban Wagner ya jagoranci yunkurin yi wa sojojin kasar tawaye a karshen watan Yunin wannan shekara. Da ma akwai rade-radin da ke cewar kwanakinsa sun zo karshe, sakamako wannan barazana da ya yi wa Putin da ke zama mafi girma a tarihin mulkinsa.

Karin Bayani: Ko akwai inginzo Rasha a juyin mulkin Nijar?

Duk da cewar shugaban kasar Belarus wanda ya ba shi mafaka ya sasanta shi da Putin din, za a iya cewa sasanci bai yi aiki ba kasancewar bayan sasancin Putin din ya janye tallafin da yake ba kamfaninsa na Wagner ta re da bukatar mayar da shi Belarus da kuma bai wa dakarunsa zabin su bi shi can ko kuma su shiga rundunar sojojin Rasha. Ko shin ya ya aka yi Prigozhin da ke sayar da abinci, ya zamo kwamandan sojoji da ke shugabantar runduna a fage daga? A shekara ta 1990 jim kadan bayan fitowarsa daga gidan yari inda ya shafe shekaru tara kan laifin fashi da makami da zamba, ya hadu da Shugaba Vladmir Putin.

Rasha | Vladmir Putin | Rundunar sojojin haya | Wagner | Yevgeny Prigozhin | Mutuwa
Shugaban rundunar sojojin hayar Wagner Yevgeny Prigozhin da Shugaba Vladmir PutinHoto: Alexei Druzhinin/AP/picture alliance

Bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet ya bude gidan sayar da abinci, inda ya yi amfani da sanayyarsa da Putin ya inganta sana'arsa. kafin ka ce wani abu gidan cin abinsa ya zama wata matattarar masu kumbar susa a mahaifarsa St Petersburg. Aminci ya shiga tsakaninsu, inda har ta kai bayan Putin ya yi nisa a mukami kamfaninsa ke dahuwar abincin manyan baki da ma shi kasa Shugaba Vladmir Putin. Prigozhin ya samu kwangiloli masu tsoka, a karkashin wannan gwamnati da ake zargin ta ga bayansa. Shugasban sojojin na Wagner ya yi karfin da ba a iya misalta wa, inda har ya samu nasarar bude kamfanin sojojin hayar da ya jagoranci yaki gami da yada farfagandar Rasha a ciki da wajen kasar.

Karin Bayani: Tasirin Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A watan Fabarairun 2022 bayan da Rasha ta kaddamar da mamayarta a Ukraine da sojojin kasar ke ta mutuwa, an ba shi damar samar da sojojin da za su taya Rasha yakin. Ya kwaso 'yan kurkukun da aka yi musu afuwa kan sharadin taimakon Moscow, duk da cewar doka ta haramta masa shiga yaki da sunan kasar. Bayan sojojin Rasha sun gaza katabuus a yakin Ukraine, rundunar Wagner ce ta yi nasarar karbe iko da birnin Bakhmut a watan Mayun wannan shekara da muke ciki, nasarar da ke zama babba a yakin da Kremlin ta kwashe sama da shekara guda tana yi da makwabciyar tata. An samu kai ruwa rana, inda har Prigozhin ya zargi sojojin Rasha da cin hanci da kuma yin makarkashiyar da ke hana su samun nasara a yakin. Kazalika, ya zargesu da cin amanar kasa da hana Wagner damar samun wasu makamai.