1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An bude makarantu a wasu jihohin kasar

October 5, 2020

A Najeriya tun bayan rufe makarantu tsawon lokaci saboda cutar Corona, gwamnatin jihar katsina dake arewacin kasar ta bude makarantun gwamnati da masu zaman Kansu a jihar domin cigaba da karatu.

https://p.dw.com/p/3jTDt
Nigeria l Schulstart - Schuleröffnung
Hoto: Yusuf Ibrahim Jargaba

Tun bayan rufe makarantu tsawan lokaci a Nigeria sakamakon cutar Coronavirus, a yau Gwamnatin jihar katsina dake arewacin kasar ta bude makarantun jihar na Gwamnati da masu zaman Kansu domin cigaba da koyo da

Sakamakon wannan Cuta ta Covid-19 wadda ta janyo rufe makarantun yasa su kansu malamai sun gaji da zaman gida abin da yasa ana komawa makarantar suka fara aiki gadan-gadan acewar Lawal Lawal Kurfi shugaban makarantar jeka ka dawo bangaren jiniya dake kofar sauri a jihar Katsina

Nigeria l Schulstart - Schuleröffnung
Dalibai a wata makarantar sakandare a KatsinaHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba

To ko wane tsari mahukuntan jihar suka yi game da yanayin zangon karatun Farfesa Badamasi Charanci shi ne kwamishinan Ilmin Jihar ta Katsina.

"Mun ba da sati uku a wannan zangon karatu. Sati biyu na farko a maimaita abin da aka yi a baya sati daya kuma a yi jarrabawa wanda shi ne zai kawo karshen zangon karatun na biyu. Sannan za a rufe zangon karatuin a ranar 23 ga watan Oktoba 2020".

Kwamishinan Ilmin ya kara da cewa za dawo makaranta a ranar 26 ga watan Oktoba domin cigaba da zangon karatu na uku har zuwa 5 ga watan Fabrairu 2021.

Dalibai dai a jihar Katsina na cigaba da nuna jin dadinsu kan bude makarantun

Domin tabbatar da cewa ana bada tazara a azuzuwa mahukunta a jihar sun raba makarantun jihar gida biyu wasu daliban su je da safe zuwa 12:30 wasu kuma su je daga rana zuwa yamma domin kare lafiyar su