An sake sukar salon mulkin shugaban Najeriya
July 16, 2019
Ba dai bako ba ne wajen rubutu na wasiku. Ya kuma aike ta ga shugabanni na farar hula da 'yan uwansa shugabannin sojoji na kasar, a bangaren tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
A baya dai wasikar tai tasiri a wajen gyara, a wani lokaci kuma ta kare a cikin kwandon shara, sannan kuma shugaban ya bugi kirjin kai karshe na gwamnati da wasikar tasa.
Kuma kama daga neman sake kiran taro na kasar zuwa ga zargin hadari da ruwan rikici na daf da fara zuba cikin kasar dai tsohon shugaban kasar ya kare tare da nuna alamar kasawa a bangaren gwamnatin da ke ci yanzu game da tsaro.
Batutuwan kuma da suka dauki hankali na kasar dake masu kallo da idanu daban daban a tsakani nay an kasar daban daban.
Alhaji Tanko Yakasai dai ya share sama da shekaru 50 yana taka rawa a fagen siyasa ta kasar kuma ya ce wasikun na Obasanjo ba sabbabi ba ne sannan kuma ba su da niyyar neman gyara lamura na kasar.
Kokarin bata suna na kare ko kuma fadi na gaskiya cikin halin rikici, Senata Umar Kurfi dai na zaman daya a cikin dattawan jihar Katsina inda rikicin kisan yake tashi da lafawa, kuma a fadarsa goyon baya da addu’a ake da bukata ba wai wasikar ta Obasanjo ba.
Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin fadar shugaban kasar da ke karatun kurma game da wasikar, da kuma Obasanjo da ke kara kwarewa cikin sana’ar ta wasika.