Amincewa da shigo da kayan abinci Najeriya
July 9, 2024Hauhawar farashin kayayyakin da ake fama da shi a Najeriyar dai, ya jefa rayuwar al'ummar kasar cikin mawuyacin hali. Gwamnatin kasar ta jima tana fuskantar matsin lamba a kan ta bude kan iyakokin kasar, domin shigo da abinci sakamakon mawuyacin hali da ake ciki na tsadar kayan abincin da aka dade ba a ga irinsa ba a 'yan shekarun nan. Cikin matakan da ministan Kula da Aikin Gona da Samar da Wadatuwar Abinci ya sanar, ya nunar bude kan iyakokin kasar da aka rufe tun a watan Augustan 2019 lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari. Kodayake ana ta murna da sanar da wannan mataki, amma masani a fanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi na ganin sai fa an sa ido sosai.
Gwamnatin Najeriyar dai ta ce ta dauki wannan matakin ne, domin samar da sauki ga alummar kasar da tsadar kayan abincin ya jefa mafi yawa cikin hali na ukuba da ma barazanar matsalar yunwa. Baya ga kayan abincin da 'yan kasuwa za su shigo da su a wannan lokaci, gwamnatin za ta shigo da ton dubu 250 na masara da alkama. A baya dai gwamnatin ta dauki irin wannan mataki, sai dai kuma ba wani tasiri da ya yi. Gwamnatin ta ce za ta yi amfani da tsarin kayyade farashin kayan abincin, domin dakile 'yan kasuwa masu mugun nufi da kan fake da irin wannan dama su ci kazamar riba. Tun kafin wannan lokaci shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya umurci jami'an kula da tattalin arziki su samar da Naira tirliyan biyu, domin shawo kan matsalolin hauhawar farashin kayayyakin.