Najeriya: An fara shari'ar 'yan Boko Haram
October 9, 2017Talla
Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce za a yi wa mutanen shari'ar ce a asirce kuma za a fara da mutum 1,670 wadanda ake tsare da su a wani sansanin soji da ke Kainji a jihar Neja da ke tsakiyar kasar. Baya ga wannan, za a yi wasu mutanen 651 shari'a a barikin Giwa da ke birnin Maiduguri na jihar Borno su din ma dai bisa zarginsu da hannu wajen tashin hankalin da kungiyar ta Boko Haram ta haddasa. Ministan shari'a Najeriya Abubakar Malami ya ce kowanne mutum da ake tuhuma na da 'yancin daukar lauyan da zai tsaya masa.