1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kama masu garkuwa da mutane

September 24, 2021

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum uku cikin wadanda ake zargi da yin garkuwa da dalibai 121 a wata makaranta a jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/40mfp
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Ba kasafai ake samun damar kama wadanda ake zargi da laifin sace 'yan makaranta da ke neman zama gagarabadau a yankunan Arewa maso yamma da kuma tsakiyar Najeriya ba.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2021 ne 'yan bindiga suka sace daliban makarantar kwana ta Bethel Baptist a jihar Kaduna, wanda har yanzu 'yan bindigar ke ci gaba da tsare 21 bayan sakin wasu 10 a makon da ya gabata.

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Frank Mba ya ce sun kuma gano bindigu tattare da 'yan bindigar. Najeriya da ke zama kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka na fama da matsalar garkuwa da mutane musaamman dalibai don neman kudin fansa, inda alkaluma ke nuna cewa daga bara an yi garkuwa da dalibai kimanin 1,400.