1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tsaro a arewacin Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 18, 2020

Al'ummomin wasu jihohi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na cikin matsanancin tashin hanakali dangane da hare-haren 'yan bindiga da suka addabe su.

https://p.dw.com/p/3dzam
Nigeria Katsina Sicherheit
Zanga-zangar kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki mataki kan matsalar tsaroHoto: DW/H. Y. Jibiya

Za dai a iya cewa tura ta kai bango, domin kuwa tuni matasan yankin arewacin Najeriyar suka fusata har ma suka dauki matakin yin zanga-zangar lumana. An dai kaddamar da zanga-zangar a jiahar Katsina, guda daga cikin jihohin da hare-haren 'yan bindigar ya fi muni, jihar kuma da ke zaman mahaifar shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Matasan dai sun sha alwashin yin zanga-zangar a dukkanin jihohin kasar domin nuna takaicinsu da kuma yin kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan da suka dace, domin tsiratar da rayuka da dukiyoyin al'ummar da ke fuskantar sata da kisa da cin zarafi da fyade a hannun 'yan bindigar.

Sai dai abin takaici, rahotanni da ke fitowa daga Tarayyar Najeriyar, sun nunar da cewa an kame jagoran wannan zanga-zanga mai suna Nastura Ashir Sharif: 'Yan gudun hijira cikin tasku