Najeriya: APC ta zabi Oshiomhole
June 23, 2018A karon farko tun bayan darewarta kan gadon mulki a cikin Tarrayar Najeriya, yayan jam’iyyar APC , mai mulki na can na babban taro na kasa da a cikinsa ake saran tabbatar da sabbabi na shugabanni da za su ja ragamar masu tsintsiyar zuwa zaben da ke tafe.
Wakilai 6800 da kuma ragowar dubun dubata na magoya ne dai suka dage wa ruwan sama da bakin kwarya, domin shiga cikin babban taron da ke zaman irinsa na farko ga jam’iyyar APC mai mulki Tarrayar Najeriya.
Wani abun da ya dauki hankali a zauren taron dai na zaman hallarar daukacin yayan sabuwar PDP, in banda tsohon gwamnan jihar Kano Senata Rabiu Kwankwaso.
Tun kafin a kammala zabe na sauran shugabanni, taro ya kai ga tabbatar da zaben tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Aliyu Oshiomhole, a matsayin sabon shugaban jam'iyyar babu hammaya a cikin wata kuri’ar murya..
Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a kokari na dinkewar jam’iyyar da kila ma samar mata damar kai wa ya zuwa nasara a zaben watan fabrairun badi.