Kokarin ceto Naira ya janyo asarar kudi
December 26, 2022Wadannan makudan kudi da Najeriyar ta yi asararsu cikin shekaru hudu dalilin manufofi iri dabam-dabam da babban bankin kasar ya rinka amfani da su, ya sanya Bankin Duniyar yin kashedi kan sakamakon da hakan zai haifar. Babban bankin Najeriyar ya kan sayarwa da 'yan chanji dala dubu 60 a kowane mako, abin da ya kai dala dala miliyan dubu takwas dari shida a shekara. Tuni wannan ya sanya kwararru a fanin tattalin arziki a Najeriyar daga 'yar yatsa, suna tambayar dalili. Babban bankin Najeriyar dai ya sha hakikancewa a kan dalilansa na daukar wannan mataki musamman na kokarin ceto darajar Naira, inda har Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta kasar EFCC ta kai samame a kan 'yan canjin kan zarginsu da sanya darajar dalar Amirkan hawa a kan ta Naira.
#b#Amma ga Mallam Abubakar Ali da ke zaman masanin tattalin arziki, kudin da aka kashe mtsawon shekaru hudu a kokarin ceto Nairar da ba ta samun tagomashi ma abin yin nazari ne. Hango uwar bari ta sanya babban bankin Najeriyar dakatar da bayar da dalar Amirkan ga kamfanonin 'yan canjin, inda a watan Yulin 2021 bankin ya sanar da dakatar da sayar da dalar ga masu sana'ar canjin. A yayinb da Bankin Duniya ke jan kunne kan illar wannan zunzurutun kudi da Najeriyar ta kashe a kokarin daidaita farashin dalar Amirkan, har yanzu babban bankin na da kofofi na musayar dalar da ya bayyana a matsayin matsala. Duk da matakai da gwamnatin Najeriyar ta dauka na katse hanzarin amfani da dalar Amirka wajen saye da sayarwa musamman biyan kudin makaranta a kasar, har zuwa yanzu ana fuskantar kalubale na auna farashin dalar da 'yan kauswa ke yi wajen sanya farashin kayayyakinsu, abinda ke haifar da tsadar rayuwa.