1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Baje kolin makamai da aka yi fasakaurinsu

September 21, 2017

Rundunar Kwastam a Najeriya ta yi baje kolin wasu muggan makamai da ta ce ta kama a daidai lokacin da ake kokarin yin fasakaurinsu zuwa cikin kasar ta tashar jiragen ruwa da ke Legas.

https://p.dw.com/p/2kUck
Waffenschmuggel Lagos
Hoto: DW/M.B.Bello

Makaman dai sun hada da bindigogi sama da dubu biyu da dari shidda da aka kama cikin watanni takwas na wannan shekara a tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island da ke Legas. Kamun da aka yi na baya bayan nan ya shigo ne daga kasar Turkiyya da suna wani kamfani wai shi James Great Oil and Gas Limited. Su dai wadannan makamai da aka kama an sanyasu ne cikin kayan bandaki da nufin badda sawu sai dai jami'an kwastam din sun bankado abinda ke ciki bayan da suka gudanar da cikakken bincike.

Lagos Port Hafen Nigeria
'Yan fasakauri kan yi amfani da tashar jiragen ruwa don shigar da muggan makamai NajeriyaHoto: AFP/Getty Images

Da ya ke bayani yayin baje kolin wadannan makamai da hukumarsa ta kama, shugaban Kwasam din Kanar Hameed Ali mai ritaya ya ce ''Najeriya ba za ta zuba ido ta na ganin yadda ake amfani da wasu marasa kishin kasa don tayar da fitina a cikin kasa kuma wadannan muggan makamai sun shigo cikin kasar ce daga Turkiyya kuma za mu zauna da jakadan kasar don tabbatar masa da cewa wadannan makaman sun fito ne daga kasarsa.''

Wannan lamari dai yanzu haka ya haifar da muhawara a Najeriya inda 'yan kasar ke tofa albarkacin bakunansu iri-iri yayin da wasu ke cike da mamaki musamman kan yadda wasu mutane suka raja'a wajen neman hargitsa kasar wannan ne ma ya sanya da dama ke cewar jami'an tsaro su kara kaimi don an karya kashin bayan masu wannan mummunar dabi'a.