Najeriya: Buhari ya gabatar da nasarorin da ya cimma
November 17, 2017Shugaban na Najeriya ya yi bitar wadannan nasarori ne gaban dumbin magoya baya da makusanta a babban birnin tarayyar kasar Abuja inda ya tabo batutuwan da suka hada da tsaro musamman ma dai yaki da ta'addanci a sassan kasar daban-daban ciki kuwa har da yankin arewa maso gabas wanda rikicin Boko Haram ya tagayyara. Gwamnatin ta Buhari dai ta ce ta samu nasarar dakile aiyyukan ta'addanci a Najeriya da kusan kashi 80 cikin 100 daga hawanta kawo yau.
Baya ga batun tsaro, shugaban ya kuma tabo yakin da gwamnatinsa ta daura da cin hanci da rashawa wanda 'yan kasar da dama ke kallo a matsayin matsalar da ta dabaibaye kasar shekara da shekaru. Wannan batu na daga cikin irin abubuwan da ke sahun gaba a cikin jerin alkawuran da da jam'iyyar Buharin ta APC ta yi a lokacin da ta ke yakin neman.
Wani abu har wa yau da shugaban ya tabo shi ne tattalin arziki inda gwamnatinsa ta ce ta taka rawa ta a zo a gani wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya din daga irin halin kunci da ya samu kansa a ciki. Yayin bitar wadannan abubuwa dai, Buharin da jama'arsa sun yi kaddamar da wani littafin da ke dauke da jeri cigaban da suke ce sun samu a watanni kusan 30 da suka shafe suna jan ragamar kasar.