Bikin karamar Sallah a Najeriya
May 13, 2021Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar da kuma gwamnan jihar Sakkwato Aminu Wazirin Tambuwal da sauran mahukuntan jiha suka sallaci tasu sallar. Mutane da dama ne dai suka halarci wannan sallah ta bana a masallatan idi dabam-dabam, kasancewar sallar bara ba a samu halarta ba sakamakon annobar cutar coronavirus.
Jawaban sarkin Musulmi da gwamna da suka saba gabatarwa, a wannan lokacin sun mayar da hankali kan muhimmancin samar da tsaro da kuma kara daukar matakan kiyaye kamuwa da cutar corona. Shagulgula dai sun kaure a sassan Najeriyar, inda a jihar Sakkwato masu dawaki da rukuma ke ta yin kara-kaina a titunan birnin, a kokarin raya al'ada da aka saba ta kai gaisuwar ban girma a fadar Sarkin Musulmi a irin wannan lokaci. Sallar dai ta bana ta samu halartar dimbin mutane da aka dauki dogon lokaci ba'a ga irin sa ba anan Sakkwato.