Najeriya: Cikas a musayar 'yan Chibok
September 17, 2016Gwamnatin Najeriya ta bude kofa ta tattaunawa da mayakan Boko Haram a kokari na ganin an sako yara 'yan Makarantar Chibok tun a shekarar 2015, sai dai kawowa yanzu shirin ceton yaran na fiskantar tangarda saboda rabuwar kai a tsakanin mayakan na Boko Haram a cewar ministan yada labarai a Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja fadar gwamnatin ta Najeriya Mista Lai Mohammed ya ce dakarun tsaro na farin kaya sun shiga tattaunawa da mayakan tun daga watan Yuli na shekarar 2015 a kokari na ganin an yi musayar yaran sama da 200. Sai dai gwamnati ta rufe ci gaba da batun a watan Agusta 2015 bayan da mayakan suka bijiro da wasu sabbin bukatu. A watan Nuwamba an sake komawa kan tattaunawar sai dai rikicin shugabanci a kungiyar ya maida hannun agogo baya.
A cewar Lai Mohammed duk da tangarda gwamnati na kokari na ganin ba ta karaya ba a kokari na kubutar da 'yan matan bayan da ake samunci gaban tuntuba ta wadanda gwamnati ta amince da su.