1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cin hanci a cikin yaki da corona

Uwais Abubakar Idris AH
September 2, 2021

A Najeriya gamayyar kungiyoyin farar hula a karkashin jagorancin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta BudgIt sun bakado gagarumin zargi na cin hanci da rashawa a cikin aikin yaki da corona.

https://p.dw.com/p/3zq54
Nigeria I Intensivstation I COVID-19
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Najeriya dai ta samu taimako a cikin kasar da ma kasashen waje na bilyoyin Naira a matsayin tallafi na annobar Covid, inda ta ce ta kasafta Naira bilyan 500 a bara a wannan fani,amma zargi na rashin fitowa a kasa a fai-fai ya sanya gamaiyyar kungiyoyinn yaki da cin hanci da rashawa da ma masu sa kai gudanar da bincike mai zurfi a wasu jihohin kasar. Inda suka ce sun fa bakado abubuwan da aka yi ba dai-dai ba da suna yaki da annobar ta Covid a Kaduna, Sokoto Delta da kuma Enugu. Alal misali a Jihar Delta an kasafta kudi Naira bilyan 50.13 da sunan yaki da cutar Covid 19 da ma tallafa wa jama'a amma bincike ya gano bilyan 4.92 ne aka yi aikin sauran kuma an yi wata hanya da su.

'Yan siyasa na jam'iyyar da ke yin mulki sune suka fi amfana da kudaden da aka karkata da sunan yaki da corona

Nigeria Covid-19 Impfung in Abuja | Dr. Eragbai Faith
Hoto: Uwais Idriss/DW

Ko da yake daga gwamnatin tarayyar Najeriyar zuwa ga jihohi dukka sun kasafta kudi domin talafa wa mutane don samun rage musu radadai na koma bayan tattalin arziki da cutar ta haifar, amma ‘yan siyasa sun yi kakagida da lamarin, inda wadanda ke jam'iyyar da ke mulki da masu goyon bayansu ne suka fi amfana, maimakon tsari na kamanta gaskiya ga kowa. Ana dai zargin gwamnatin da rufa-rufa a kan daukacin lamarin inda aka bakado  wannan barna ta zargin rub da ciki ta hanyar ci da gumin jama'a da suna tallafi na annobar. A bisa abin da aka gano ya nuna bukatar kawar da rufa-rufa da kamanta adalci daga bangaren jami'an gwamnati a daya daga cikin matakan rage matsalar cin hanci da rashawa musamman a fanin kula da lafiyar jama'a.