Nigeriya: Cutar Lasa ta bulla a Lagos
August 9, 2017Talla
A cewar Farfesa Chris Bode, babban Daraktan asibitin koyarwa na jami'ar birnin Lagos inda aka kwantar da marasa lafiyar, cutar ta yi nisa a jikin mutanen biyu da aka kwantar kuma sun yi iyakar kokarin ceto su amma hakan bata samu ba. Daya daga cikin wadanda suka mutun wata mata ce mai shekaru 39 da haihuwa kuma ta na dauke juna biyu. Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bayyana cutar ta zazzabin Lasa a matsayin cutar da ke cikin dangin cutuka irin su Marburg da kuma Ebola, kuma cutar ta samu wannan suna ne daga wani yanki na arewacin Najeriya inda aka gano cutar a karon farko a shekara ta 1969. Birni na Lagos dai na da jama'ar da yawanta ya kai miliyan 20.