1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake dage zaman majalisa a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 24, 2018

A Najeriya majalisar dokokin kasar ta sake dage zamanta da za ta dawo a ranar Talata, har zuwa tara ga watan Oktoba mai zuwa, a daidai lokacin da ake nuna damuwa a kan rashin amincewa da kasafin kudin hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/35Q2I
National Assembly in Abuja, Nigeria
Hoto: DW

Tuni dai 'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriyar suka ce akwai dai wani dalilin da ya sanya majalisar sake dage zaman nata. Jan dagar da aka yi a tsakanin 'ya'yan jamiyyar APC mai mulkin da ta PDP ta 'yan adawa a majalisar dokokin, na kara fitowa fili musamman biyo bayan canza shekar da shugabanin majalisun biyu suka yi, abin da ya sanya shakku a kan duk wani dalili na dage komawar majalisar da aka shirya.

Batun kasafin kudin hukumar zaben Najeriyar da ke gaban majalisun dai shi ne yafi daukar hankali da ma jefa alamar tambaya a kan abin da ke faruwa a majalisar dokokin Najeriyar. To sai dai ga dan majalisa Musa Sarkin Adar da gangan shugabanin majalisar ke yin haka. A yayin da ake ci gaba da wannan takaddama kwararru na nuna damuwar illar da wannan zai yi ga daukacin dimukurdiyyar Najeriyar, musamman ma dai shirin gudanar da zabe. A yayin da 'yan majalisar musamman shugabanninta da a yanzu suka koma jamiyyar adawa kuma basa ko mafarkin barin mukamansu ke ci gaba da jan kafa a kan komawar majalisar, da alamun dimukuradiyyar kasar da al'ummarta ne za su ci gaba da dandana kudarsu.