Najeriya: Ana dambarwar siyasa Jihar Rivers
November 5, 2023Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da wasu dattawan Jihar Rivers da kuma wasu gaggan 'yan jamiyyar PDP su sa baki domin sasanta rikicin da ke tsakanin gwamna mai ci Siminilayi da uban gidansa tsohon gwamna Nyesom Wike amma ga alama lamarin ya ci tura, abin da yan jihar ke cewa ba su ji dadinsa ba.
Dama dai rikicin gaggan biyu na jihar ta Rivers, Gwamna Siminilayi Fubara da tsohon gwamnan Nyesom Wike ta dade tana naso, sai a makon da ya gabata ne ya bayyana.
Rigimar dai ta kai ga fito na fito da magoya bayan su, inda aka yi ta zanga zangar da ta kai ga kokarin auna gwamnan da binduga da aka nuna jami'an 'yan sandan jihar sun yi, tare da yi masa feshin ruwan zafi.
Karin Bayani:Rigimar 'yan siyasar jihar Rivers ta munana
Ana tsaka da rigimar kuma gwamnan ya tsige masu mubaya'a ga tsohon gwamna Wike daga mukamansu sannan an sauya shugabancin majalisa, inda har yanzu majalisar jihar ke da shugabanci guda biyu. Ko da yake shugaba Tinubu, da manya 'yan jamiyyar PDP da ma dattawan jihar Rivers sun shiga tsakanin amma har yanzu baa kai karshe ba.
Wani babban batun dubawa shine, tun bayan zaben Siminilayi Fubara a matsayin Gwamna, wani dattijon iahar ya ja wa gwamna kunne kan Nyesom Wike.
Nyesom Wike dai tuni ya bayyana matsayinsa cewar shi ba ya saurara wa duk wani da ke kokarin tumbuke tushensa na siyasa, sannan gwamna Fubara a nasa bangaren, da alamu ya dauki aniyar tsayawa da kafafunsa, wanda hakan ke nufin rigima ba ta kare ba, lamarin kuma da jama'ar jahar ta Rivers ke cewa ba sa jin dadin hakan.
Wasu 'yan jihar dai na cewa ya kamata Ministan Abuja Nyesom Wike ya bar Gwamna Fubara ya yi aikinsa domin sun fara ganin ayyuka na ci gaba ta fannin ciyar da ma'aikata gaba ga daukar ma'aikata, sannan ayyukan raya kasa sun fara kaiwa kananan hukumomi.