1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wike da Fubara sun buda sabon babin rikicin siyasa

Muhammad Bello AMA
October 30, 2023

Tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike da gwamna mai ci Fubara sun buda wani sabon babin rikicin siyasa bayan da magoya bayansu suka shafe dare suna harbe harbe.

https://p.dw.com/p/4YCCt
Nigeria I Ezenwo Nyesom Wike
Tsohon gwmnan jihar Rivers Ezenwo Nyesom WikeHoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Wannan yanayin na tashin hankalin bayan samun takar da tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da uban gidansa na siyasa Ezenwo Nyesom Wike da aka nunar cewa ya shara masa mari. Rigimar ta yi dalilin kokarin majalisar na tsige gwamnan wanda hakan ya ci tura, ko da yake an tsige wasu kusoshin majalisar tare da cinnawa majalisar wuta.

Karin Bayani: Jam'iyyyar PDP na cigaba da fuskantar rikicin cikin gida

Wasu magoya bayan gwamnan sun fito sun gudanar da zanga-zangar cewar ana neman halaka gwamnan da dora alhakin haka kan tsohon gwamnan RiversNyesom Wike, kamar yadda wani daga cikin masu zanga-zangar ke cewa "Jami'an tsaro ne ke kokarin halaka mana gwamna, kuma mu muna tare da shi, su kashe mu gaba daya, Wike ya zo ya kashe mu, ba wai yau mu ka fara ganin wannan rikicin ba, muna son duniya ta sani ta kawo mana dauki, mu Siminilayi Fubara ne muka zaba ba wani ba."

Gwamna Siminalayi Fubara ya sake bayyana

Magoa bayan 'yan siyasa da ke rikici da juna a siyasar Rivers
Magoa bayan 'yan siyasa da ke rikici da juna a siyasar Rivers Hoto: Reuters/Afolabi Sotunde

Gwamna Siminiyi Fubarada ya yi batan dabo a farko ya sake bayyana daga bisani inda ya yi wata ganawa da manema labarai a ciki ya yi zargin cewar jami'an tsaro sun rika auna shi da bindiga suna kokarin halaka shi, inda ya bayyana cewa "Daga abubuwan da na gani har jami'an tsaro na bin umarnin tsohon Gwamna Nyesom Wike suna auna ni da bundiga, kuma suna son harbi na ta yadda zan zama tarihi".

Karin Bayani: An dakatar da tattara sakamako a Jihar Rivers

Tun bayan daure gindin zaben na Siminilayi Fubara a matsayin gwamnan Jihar Rivers a zaben 2023 da Nyesom Wike ya yi, daga dukkanin alamu ba'a dade ba tafiyar ta fara tsami, sakamakon nade-naden mukamai da kuma ayyukan gwamnati, wannan rigimar da ta bayyana a fili yanzu dama ba sabuwa ba ce a Jihar Rivers, Allah ne kadai ya san karshen ta.