1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Damuwa kan rashin siyasar akida

September 3, 2024

A yayin da jam'iyu na adawa a Najeriya ke tunnin hada kai da nufin tunkarar masu tsintsiyar APC a nan gaba, miliyoyi na yan kasar na nuna damuwa kan rashi akidar da ke zaman ruwan dare ga 'yan siyasa

https://p.dw.com/p/4kEgG
Bildkombo Nigeria Wahlen | Peter Obi, Bola Tinubu (M), Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Babbar damuwa a halin yanzu na zaman makomar jam'iyyun adawa a tarayyar Najeriya dama burin nasara a zabukan kasar da ke gaba. Abun da ke daukar hankalin jam'iyyun adawa a kasar da ke fadin sun bude tattaunawa da nufin hada kai domin tunkarar jam'iyar APC da ke mulkar Najeriyar a halin yanzu.

Rikicin cikin gida ya mamaye kusan daukacin manyan jami'iyyun da ke adawa a kasar, haka kuma burin mulki na kara baiyana a tsakanin masu adawar a Najeriya. Alal ga misali Wike da ke ikirarin zama cikin PDP na yakar gwamnonin jam'iyyar a cikin rigar  APC mai mulki.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar

Ita ma jam'iyyar labour ta yi nisa cikin batun rabuwar kai a tsakanin masu kodagon da ke tunanin kafa jam'iyyar tun daga farko, da kuma masu goyon Peter Obi da suka yi nasarar daukar jam'iyyar ya zuwa sabon matsayi.

Batun siyasar kudi a tunanin Sanata Ibrahim Musa kazaure da ke zaman tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, na zama barazana da ke iya rushe tunanin hada kan jam'iyyun adawar.

‘‘Mutanen da ka sani a yanzu, kowa in ka bashi kudi, kudi ne kat, kuma in ka shiga siyasar kudi, to sai a hankali. Kuma mutum biyu a Najeriya ba'a rigimar kudi da su, da Tinubu da Ali Modu Sherif, domin za su fidda kudi su yi abun da suke so.‘‘

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya
Majalisar dokokin tarayyar NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Siyasa ta akida, ko kuma kokarin neman cika burin son rai, masu adawar na kallon dama cikin  rikicin tattalin arziki dama tsaron da ke zaman mai girma cikin kasar a halin yanzu.Kuma da kamar wuya kudin su yi tasiri a kokarin neman sauyi a tunanin Shehu Gabam dake zaman shugaba na jam'iyyar SDP na kasa.

‘‘A siyasance da bude ido a siyasa a Najeria a yau, ba wanda zai tilasta musu. Kowa ya fada cikin wuya , kowa ya san masifar da ya fuskanta. Mutane suna iya karbar kudi, amma dai miliyoyin yan Najeriy basu shirin sake fadawa cikin rikicin da suka shiga. Ko sun karbi kudin ba za su sake fadawa cikin irin abun da ya basu wuya ba,''

‘‘Kama daga delegate da suka karbi dala yayin zabukan fidda gwani, ya zuwa talakawan da suka kare da taliya domin zaben gama gari, shekara guda a tarayyar Najeriya ta sauya da dama cikin batun tattalin arziki da siyasar.

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya
Majalisar dokokin tarayyar NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

To sai dai kuma har yanzu da sauran tafiya a tunanin farfesa Kamilu Sani Fagge da ke zaman kwarrare a siyasar da kuma  ya ce da kamar wuya ake iya banbance masu adawar da masu tangadi cikin dadin mulkin.

‘‘In da za ka dauki tsarin mulkin jam'iyyun ko kuma abun da suka sa a gaba za ka ga duk kusan abu daya ne. Wannan shi yasa za ka ga wadanda suke fadar a hada kan da suna PDP daga ba su koma APC wasu kuma sun shiga wasu jam'iyun.‘‘

Duk da cewar miliyoyin al'ummar kasar na tsaka a cikin neman sauyi, sannu a hankali suna dada dawowa daga rakiyar masu takama da siyasar da bakunasu ke zaman daban da karatun da ke tsakiyar zuciya