Najeriya: Shugaban babban banki ya shiga hargitsi
June 16, 2023A 'yan watannin da suka gabata, Emefiele yana daya daga cikin manyan mutane masu karfin fada aji ba wai a Najeriya kadai ba har a duka a Afirka baki daya. Ya jagoranci babban bankin kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kuma ya nemi zama shugaban kasa.
Amma a yau mai shekaru 61 a duniya, Emefiele yana gidan yari. Emefiele shi ne fitaccen mutum na farko da sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda ya hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya fara da shi a kokarin cika alkawarinsa na tsaftace kasar ta yammacin Afirka daga matsalar cin hanci da rashawa da kuma almundahana da yayi wa kasar katutu
An dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, tare da ba shi umarnin mika ragamar bankin ga mataimakinsa, Folashodun Adebisi Shonubi.
Kama shi ya fi haifar da cece-kuce, inda aka yi ta yada jita-jita game kan kamun sa. Da farko dai hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ce bata san komai ba, hukumar da ta sha fuskantar zargi na bin umurnin gwamnati a baya.
Ita kuwa jaridar Der Taggesspiegel sharhi ta yi ne kan kokarin da kasashe makwabta ke yi na gano bakin zaren warware rikicin siyasa da madafan iko da kasar Sudan ta tsinci kanta a ciki.
Fada da tashin bama-bamai sun yi barna a babban birnin kasar watau Khartoum. Dubban daruruwan mutane sun tsere, tun bayan barkewar rikicin tsakanin sojoji da mayakan sa-kai, rikicin da ke ci gaba da daukar hankalin kasashen duniya.
A lardin Darfur da ke yammacin kasar, shigar mayakan kabilu cikin rikicin ya kara ruruta wutar rikicin tare da haifar da fargabar fadan na iya kara yaduwa kuma ya dauki lokaci.
Rayuwar al'ummar kasar da ke yankin arewa maso gabashin Afirka dai na cikin mummunan yanayi na karancin abinci da sauran kayayyakin bukatu da suka hadar da ruwa da wutar lantarki da magunguna.
A taron da kungiyar hadin kan kasashen gabashin Afirka IGAD ta saba yi a kasar Djibouti, kasashe takwas mambobin kungiyar sun amince da wata taswirar warware rikicin.
Nan ba da jimawa ba shugaban mulkin sojan Mali zai yi sabon kundin tsarin mulki, da haka ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude labarinta kan kuri'ar raba gardama da ake shirin gudanarwa a kasar ta yammacin Afirka.