Kyamar 'yan Najeriya a Afirka ta Kudu
September 4, 2019Masu zanga-zangar dai sun rinka yin kuwwa a yayin da suka yi dafifi a gaban katafaren shagon Shoprite da ke unguwar Lugbe a Abuja, suna kona tayoyi da jifan motoci da duwatsu, a kokarinsu na afkawa shagon da nufin yin barna, abin da ya haifar da artabu da masu zanga-zangar da suka rinka jifan 'yan sandan da ma 'yan jaridu da duwatsu, inda aka kai ga raunata wasu daga cikin mutane a wurin. 'Yan sandan dai sun mayar da martani ta hanyar jefa musu hayaki mai sanya hawaye.
Tuni dai ministan kula da birnin Abujan Muhammad Musa Bello ya fitar da sanrawa, yana neman masu zanga-zangar su kwantar da hankali. Da alamu dai dangantaka tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudun ta kama hanyar yin tsami domin Najeriyar ta sanar da ficewa daga taron tattalin arziki da za a yi a Kasar Afrika ta Kudun, kana ministan kula da harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya ce Najeriyar ta bukaci jakadanta da ke Afika ta Kudu ya dawo gida domin tuntubar juna.