Filato na neman taimakon magance rikicin jahar
June 27, 2018Gwamna Lalong ya yi wannan kira ne a wata ganawa da shugaba Buhari ya yi da wakilan al'umomin Filato a yammacin jiya a Jos. Wakilan al'umomin Fulani da Berom, tare da shugabanin wasu kabilun jahar, sarakunan gargajiya da shugabanin addinai ne suka halarci zaman. Lalong a jawabinsa ya nuna damuwa kan irin halin da jahar Filato ke neman komawa.
Da ya ke mayar da martani, shugaba Buhari ya ce baya barci kan matsalar tsaro da tashe-tashen hankula da ke aukuwa a sassan kasar daban.
Shugaban rikon mulkin karamar hukumar Riyom, Emmanuel Danboyi Jugul, ya ce abinda ke haddasa rikici a jahar a duk lokacin da aka sami tashe-tashen hankula tsakanin kabilun Fulani da Berom matafiya dake bin hanya tsakanin Abuja zuwa Jos, kan shiga halin firgita sakamakon yadda wasu matasa kan tsare hanya suna cin zarafin su.
A wata ganawa da muka yi da shi kakakin rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jahar Filato Major Adamu Umar ya tabbatar da cewa, yanzu hankula sun soma kwanciya, inda jami'an tsaro ke zirga-zirga ta sama da kasa a kauyuka da a ka fi samun damuwa don tabbatar da doka da oda.