Najeriya: Hari a gidan yarin Imo ya janyo dar-dar a jihar
April 6, 2021Balle wannan gidan gyaran hali na Owerri da yanzu aka tabbatar 'yan bindigar haramtacciyar kungiyar rajin ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra bangaren IPOB ne suka aikata, ya yi jallin tserewar daurarru ma su kanana da manyan laifuka su kimanin 1844. Kuma har yanzu jami'an gidan na gyaran hali na ci gaba da kokarin daukar matakan da za su kai ga dawo da wadannan daurarru da yanzu ake ganin fantsamarsu cikin jama'a ba karamin hadari ba ne.
'Yan bindigar na kungiyar ta IPOB dai, an nunar sun yi amfani da manya-manyan makamai wajen balle wannan gidan gyaran hali.
Mr James Madugba, shi ne mai magana da yawun gidan gyaran halin na Owerri kuma ga abin da yake cewa.
"Ka duba irin barnar da aka yi, ka duba yadda aka bankawa motoci da ma ginin gidan gyaran halin wuta, da haka nake tabbatarwar cewar yayin da muka kammala bincike za mu gabatarwa da duniya cikakken bayani kan wannan al'amari."
Dangane da halin zaman zullumi na karakainar daurarrun da suka tsere daga gidan na gyaran hali, wanda kuma cikin su akwai masu kisan kai, da masu shan jini 'yan kungiyoyin asiri, da kuma 'yan fashi da makami, jamaa da dama musamman ma mazauna birnin Owerri, sun bayyana damuwarsu na wata kila gararin da ka iya biyo ba yan ballewar gidan gyaran halin na Owerri.
Tuni dai tawagar da babban Sifeto-Janar na 'yan sandan Najeriya ya aika jihar ta Imo suka gano cewar 'yan bindigar na IPOB sun yi awon gaba da makamai a sakamakon wannan hari kan hedikwatar ta 'yan sanda.
Karin bayani: Najeriya: Kama masu rajin kafa kasar Biafra
Gwamnan jihar ta Imo Hope Uzodinma kan wannan hari ya tabbatar cewar manufar wadanda suka kai wannan hari ita ce su sa tsoro a zukatan mutane.
"Ina son tabbatar muku da cewar manufar harin ita ce a sa tsoro a zukatan mutanem mu, amma kuma ina tabbatar muku cewar, gwamnati za ta hada kai da rundunonin tsaro da nufin yi wa wannan tufkar hanci, kuma tuni na kaddamar da wani kwamitin bincika yadda wannan al'amari ya faru tare ma da gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki da ma wadanda suka saka su."
Yanzu dai don kaucewa yiwuwar afkuwar wannan al'amari a wasu jahohin na kudu, gwamnatin jihar Abia ta ce ta sa dokar hana fita daga karfe goma na dare zuwa shida na safe, sannan rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta nunar cewar ta shirya tsaf kan duk wani irin tunzuri da kungiyar rajin Biafra ta IPOB din ka iya haifarwa a jihar.