Najeriya: Ina kudaden fansa suke shiga?
January 22, 2024Akalla barayin daji 29 ne wata sabuwar rundunar 'yan sanda ta musamman suka kama a makon da ya shude a Abuja. A wani abin da ke nuna karuwar nasarar jami'an tsaron tarrayar Najeriyar da ke fuskantarin matsin lamba daga 'yan kasar.
Sai dai duk da ikirarin biyan kudaden fansa a bangaren iyalan mutanen da 'yan binga suka yi garkuwa da su in banda tarin makamai, babu abin da aka samu a wajen barayin dajin da ke hannu a yanzu.
Karin Bayani: Najeriya ta yi gargadi kan biyan kudin fansa
Kusan Naira mliyan 700 ne dai aka nema, kuma iyayen wasu 'yan matan da aka kama a Abuja suka ce suna bayar da wani kaso, kafin kaiwa ga sakinsu cikin karshen mako
Ana dai kallon karuwar sullebewar miliyoyin Nairori na kudaden fansa da ake kaisu daji amma kuma daga dukkan alamu suka sake samun hanyar zuwa cikin biranen kasar.
Dokokin hada hadar bankuna a Najeriya dai sun tanadi bankuna su mika rahoton ajiyar da ta haura Naira miliyan biyar a lokaci guda a asusun ajiyar mutun guda, da Naira miliyan 10 a asusun kamfani. Dokokin kuma da daga dukkan alamu basa aiki a kasar a halin yanzu a fadar Kabiru Adamu, kware kan batun tsaro a Najeriyar.
Karin Bayani: Sojoji sun kashe 'yan bindiga akalla 100 a arewacin Najeriya
Akalla bankuna biyu ne dai aka samu da laifukan karbar kudaden satar al'umma a tarrayar Najeriya in da 'yan kasar suke biyan daruruwan miliyoyin Nairori domin samun yanci.
Dr Surajo Yakubu kwarrare wajen bin diddigin kudaden haramun ya ce hankalin bankunan Najeriyar ya rufe zuwa neman riba maimakon kare muradun 'yan kasar da ke ji a jiki.
Ko bayan al'ummar kasar da ke ji a jiki, neman fansar na kuma dakile kokarin Najeriyar na gaiyatar bakin da ke da niyyar zuba jari domin amfanin 'yan kasar da ke fadin ba dadi yanzu haka.