1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Biafra sun fasa kauracewa zabe

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2019

Kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta janye matakin kin yin zabe bayan rattaba hannu kan amincewa da wasu kudurorinsu da wasu jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya suka yi.

https://p.dw.com/p/3DSTP
Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Hoto: DW/K. Gänsler

Babu tabbacin da wadanda kungiyar ta cimma yarjejeniyar, amma ana danganta matakin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP. 'Yan Biafra dai sun dade suna da burin samun kasa mai cikakken 'yanci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar, wannan ya sa suka umurci magoya bayansu da su kauracewa zaben 2019.

Kungiyar na son amfani da wannan lokaci domin gudanar da zabukan raba gardama, da nufin kafa kasar Biafra, sai dai shugaban kungiyar Nnamdi Kanu ya bar Najeriya tun bayan da sojoji suka kai samame gidansa a watan Satumbar shekara ta 2017.