1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan zai iya yin takarar shugaban kasa

Binta Aliyu Zurmi
May 27, 2022

Kotu a Najeriya ta bai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan damar yin takarar kujerar shugabancin kasar a zaben 2023 da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4ByUg
Nigerias Präsident Goodluck Jonathan
Hoto: AP

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa wata babbar kotun kasar da ke zamanta a Yenagoa babban birnin jahar Bayelsa, ta yanke hukuncin da ke amince wa tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan tsayawa takara a zaben shekarar 2023 da kasar za ta yi. 

Sai dai har ya zuwa wannan lokaci tsohon shugaban bai bayyana ko zai yi takara a zaben da ke tafe ba, a baya gamayyar kungiyoyin arewacin kasar sun saya mishi tikitin takara, amma kuma daga bisani ya nesanta kanshi da hakan.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da al'umma a kasar ke bayyana shakku ko Mista Jonathan zai iya yin takara. A shekarar 2018 ne shugaban kasar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a gyaran fuskar da aka yi wa dokar da ta takaita wa mataimakin shugaban kasa da ya maye gurbin shugaba ko dai ta hanyar mutuwa ko kuma a sabili da wani rashin lafiya na karasa wannan wa'adi da kuma yin wani wa'adi guda daya kacal, gyaran dokar da wannan kotun ta ce, bai shafi Ebele Jonathan ba.