1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kalubalen yan kasa su karbi allurar corona

January 29, 2021

Alamu na nuwa cewa akwai babban aiki a gaban mahukuntan Najeriya wajen shawo kan miliyoyi 'yan kasar da dama wadanda ke jan kafa wajen karbar shirin allurar rigakafin mai tasiri. 

https://p.dw.com/p/3oazV
Karikatur Die 2. Corona-Welle in Nigeria

A yayin da sannu a hankali tarayyar Najeriya ke kokarin cika burin wadatar da kasar da allurar rigakafin  Covid19, daga dukkan alamu babban aikin da ke gaban mahukunta shi ne shawo kan miliyoyi na yan kasar wadanda ke jan kafa ga shiga cikin shirin allurar rigakafin

Kama daga karo karo, ya zuwa cinikin kudi dama wani bashi dai, tarrayar Najeriya tai nisa a kokarinta na samun allurar rigakafin Covid19 ga al'umma.

Kuma ko bayan allurai 100,000 na kamfanin BionTech- Pfizer, ministan lafiyar kasar ya sanar da samun karin allurai miliyan 41 da kasar ke fatan kaddamar da aikin rigakafin a kowane lokaci cikin watan Fabrairu.

dai kuma babban kalubalen da ke gaban masu mulki na zaman shawo kan 'yan kasar da tuni suka fara nuna alamun tutsu bisa mika kansu a yi musu allaurar wanda kasashen duniya da dama ke yi wa kallon matakin kawo karshen barazanar cutar.

AstraZeneca - Impfstoffhersteller
Allurar AstraZenecaHoto: Frank Hoermann/Sven Simon/imago images

'Yan kasar dai na yiwa rigakafin kallon kokari sanya musu sinadarin dake iya yin illa ga rayuwarsu dama makoma a gaba, a yayin kuma da wasu ke mata kallon yunkurin cika burin wani kamfen din turawan mulkin duniya.

Su kansu gwamnonin arewacin kasar na zaman tunga ta tunanin ba halin amincewa na zaman zakaran gwajin dafin da nufin cika burin sauya tunanin al'umma. Simon Lalong gwamnan jihar Filato kuma shugaban gwamnonin arewacin kasar na fadin cewa basu da niyyar kyale c igaba da asarar rayukan al'umma da suna na adawar allurar rigakafin.

Koma ya zuwa ina gwamnonin ke shirin zuwa da nufin shawo kan al'umma dai, da kyar da gumin goshi da kuma tsoma bakin sarakuna da malaman addinai, kafin a iya samo kan iyaye su amince a yi wa 'ya'yansu allurar shan inna.

Nigeria Abuja | Prsident Muhammadu Buhari ernennt Ibrahim Gambari zum Stabschef
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/Nigeria Presidency

To sai dai kuma a wannan karo kuma a fadar Dr Umar Tanko dake zaman kwarrare a harka ta lafiyar al'umma, adawa da rigakafin na iya kaiwa ga yin hannun riga tsakanin 'yan kasar da cika burika da dama har da na addini.

A kimiyance dai ana da bukatar samun akalla kaso 70 cikin dari na daukacin al'ummar tarrayar Najeriyar sama da Miliyan 200 kafin iya tabbatar da kariyar da ake da bukata cikin kasar a fadar Dr Ado Mohammed da ke zaman tsohon shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko dake jagoranatar rigakafi a kasar.

Rashin isowar allurar cikin kasa  har ya zuwa yanzu dai ya sa mahukuntan gaza sanya ranar kaddamar da aikin allurar cikin kasar dake kallon karuwa ta yaduwar annobar a ko'ina.

To sai dai kuma fadar gwamnatin a Abuja na kallon yiwuwar sake killace wasu sassa na biranen Legas da Abuja dan ufin rage karfin  yaduwar annobar da ke kara yawa a cikin kasar a halin yanzu.