Dakon sakamakon zabe a Kogi da Bayelsa
November 17, 2019Tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsan, inda ko baya ga batun makara da ya zargi jami'an hukumar INEC da shi, tsohon shugaban ya kuma gabatar da korafe-korafe kan yadda zaben shi kansa ya gudana, lamarin da ya kira mai da janyo nakasu ga tafiyar dimukuradiyya da ma tsarin zabuka a kasar.
Wakilinmu na yankin Nija Delta Muhammad Bello da ke sa ido kan yadda ake gudanar da zaben, ya ruwaito cewa wasu mutane sun gudanar da zanga-zanga a wani yunkuri na nuna rashin jin dadinsu kan mutanen da suka mutu a yayin zaben.
Rahotanni daga Jihar Kogi kuwa na nuni da cewa Hukumar Zaben Najeriyar INEC ta sanar a shafinta na Twitter cewa wasu ma'aikatanta 30 sun bace, tun bayan rufe runfunan zaben da ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata, koda yake daga bisani hukumar ta yi amai ta lashe inda ta ce ma'aikatan nata sun dawo babu abin da ya same su, kana tun asali ma ba su bata ba.