Karancin kayan aiki ga sojojin Najeriya
November 2, 2021Kama daga sashen arewaci ya zuwa na kudancin kasar dai, sojojin sun game ko'ina a kokarinsu na kwantar da hankulan al'umma. Daga hadarin daji zuwa harbe kunama, sojojin Najeriyar sun yi nisa a kokarin danne 'yan ta'addar Arewa maso Gabas da 'yan awaren Biafra, ko bayan barayin shanu da mutane. To sai dai kuma daga dukkan alamu karfi yana shirin karewa, ga dukkan alamu kuma aikin na neman ya wuce da sanin mai yinsa.
Karin Bayani: Hari a kan jirgin kasa ya fusata 'yan Najeriya
An dai ruwaito babban hafsan tsaron kasar Janar Lucky Irabor na fadin suna ji a jiki a kokarin samar da zaman lafiya a ko'ina cikin Tarayyar Najeriyar. Janar Irabor dai ya ce sojojin na ko'ina cikin jihohi na kasar 36, duk da rashin yawa da karancin kayan aikin da ya dauki rundunar zuwa tsaka mai tsananin wuya. Kalaman babban hafsan Najeriyar dai na zuwa a lokacin da yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar ke dada komawa wani sabon filin daga, bayan alamun nasarar kare masu ta'addan Boko Haramun da ke gabas da 'yan uwansu barayin shanun da suka adabbi yammaci da ma tsakiyar kasar.
Yawa na bata kashi a tsakanin 'yan IPOB da kuma sojojin Tarayyar Najeiryar na ta'azzara, kuma ko a wannan mako kakakin tsaron kasar Birgediya Janaral Onyema Nwachukwu ya fitar da irin girman rikicin da ke dada kare karfin sojan a sassa dabam-dabam cikin kasar. Sannu a hankali dai sojan na dauke aikin 'yan sandan da ke neman komawa kallo a cikin jan aikin na tsare dukiya da rayuwar al'umma ta kasar. To sai dai kuma duk da karuwa ta makaman da suka hada da wasu motocin yaki 60 da kasar ta sayo daga Chaina, ko bayan jiragen Super Tucano daga Amirka dai, karuwar aikata laifin na neman bankara sojan da yawansa ke raguwa.
Karin Bayani: Harin ta'addanci kan sojojin Najeriya
Sojan dai sun shige gaba sannan kuma sun mai da jami'an 'yan sanda 'yan kallo cikin tafiyar da ba ta nuna alamun haske ga masu mulki na kasar. To sai dai kuma komai rukukin rikicin, kuma a tunanin Kyaftin Abdullahi Bakoji da ke sharhi kan batun tsaron, korafin sojojin Najeriyar bai dace da irin yanayin kasar yanzun ba. Akwai dai tsoron ta'azzarar rashin tsaron na iya shafar babban zaben kasar da ke tafe kasa da wattani 18, alamun kuma da ke kara fitowa fili da irin rikicin daya mamaye jihar Anambra da ke zaben gwamna a cikin karshen mako.