1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari a kan sojojin Najeriya

March 24, 2020

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram bangaren ISWAP ne sun yi wa wata tawagar sojojin Najeriya kwanton bauna, inda ake fargabar sun halaka sojoji masu yawa.

https://p.dw.com/p/3ZxYH
Symbolbild | Soldaten | Kamerun
Sabon hari ya halaka sojoji masu yawa a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Rahotanni sun nunar da cewa sama da sojoji 70 ne ake zargin sun halaka a harin, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata kana wasu kuma suka yi batan dabo. 
Wadannan sojojin da su ka gamu da ajalinsu na aikin sintiri ne da kakkabe mayakan Boko Haram din, inda bayan fitarsu daga Maiduguri suka shiga wasu sassan jihar Yobe inda su ke bin wuraren da ake zaton akwai maboyar mayakan Boko haram domin yakar su. A kan hanyarsu ta komawa ne su ka gamu da kwanton baunar mayakan na Boko Haram a wani kauye da ake ce masa Gorgi da ke cikin karamar hukumar Konduga da ke kan iaykar jihohin Borno da Yobe.

Batan dabon jami'an sojoji

Mayakan dai sun harba rokoki ne kan wata mota da sojojin ke ciki, inda bayanai suka nuna cewa motar ta kama da wuta, nan take kuma wasu sojojin suka kone kana suka budewa wadanda suke neman tsira wuta ta hanyar kan mai uwa da wabi.

DW Still Boko Haram kill 65 people at funeral in Nigeria
Harin kwantan bauna ga sojojin Najeriya

Wasu daga cikin jami'an tsaro da su ka tsira daga harin wanda kuma su ka yi aikin kwaso gawawakin ne suka sanar da afkuwar lamarin, inda szuka ce sun kwashe gawarwaki sama da 70, baya ga wadanda suka jikkata. A cewarsu akwai jami'in soja mai mukamin kanal guda daya da kuma masu mukamin manjo guda biyu da masu mukamin laftanar sama da guda daya da kuma wasu kwamandoji da abin ya rutsa da su.

Waye ke da alhakin harin?

Shi ma wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaye sunansa ya ce sun kwashi sojoji kimanin guda 50 kuma akwai saura da har yanzu ba su iya zuwa dauko su ba, inda wasu kuma ma ake fargabar mayakan sun tafi da su. Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin koda yake ya yi kama da irin wadanda kungiyar Boko Haram ta saba kai wa sojojin. Suma a nsu bangaren sojojin Najeriyar, ba su gaskata ko musanta wannan labarin ba. Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai wa sojojin Najeriyar, tun wanda aka kai a garin Metele a shekara ta 2018 da aka halaka sojoji masu yawa.