1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: NNPC ya yi karin kudin man fetur

May 31, 2023

Kamfanin man fetur na tarayyar Najeriya NNPC ya tabbatar da yin kari a kan farashin litar mai a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/4S28l
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Cikin wata sanarwar da ya watsa ta shafinsa na Twitter, kamfanin NNPCn ya ce ya yi karin ne domin dacewa da halin da ake ciki a harkokin makamashin kasar, bayan sanarwar janye tallafin mai da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar kama mulki a ranar 29 ga wannan wata na Mayu inda ya sanar da matakin tsame hannun gwamnati daga bayar da kudin tallafi ga man fatur.

A sanarwar kamfanin NNPC ya kuma nemi afuwa daga ‘yan Najeriya, saboda wahalhalun da karin zai iya haifarwa a harkokinsu na yau da kullum.

Yanzu dai farashin litar man fetur a Najeriya zai kama ne daga Naira 500 zuwa abin da ya yi sama, inda tuni ma wasu gidajen mai a Abuja suka daga farashinsu zuwa Naira 537.