Karuwar ayyuka 'yan aware a Najeriya
April 15, 2024Kama daga Niger-Delta Volunteer Force ta tsagerun yankin Niger-Delta ya zuwa ga IPOB dake neman kasar Biafra dai an dauki lokaci ana fafutuka a cikin neman karshen zama wuri daya tsakanin sassan tarayyar Najeriyar daban daban.
To sai dai kuma bullar kungiyar Yoruba Democratic Nation data aiyana kafa sabuwar kasar Yarabawa na shirin sauya da dama a cikin kasar da ke tunanin kare gwagwarmayar ta aware a lokaci na kankane.
Sake tashin tokar ta aware daga kabari dai na kara fitowa fili da irin girman rikicin dake gaban mahukuntan tarrayar Najeriyar da ke ta kokawar tunkarar rashin tsaro da tattali na arziki cikin kasar.
A yayin da ragowa na kasar ke zaman jira na martanin yan mulkin bisa ikirarin ballewar yarabawar, dai matakin na Ibadan dai na zaman babban dama ga shugabanni na kabila ta Igbo dake ta fafutukar neman sakin jagoran awaren yankin Nmandi Kanu.
Su kansu masu tunanin na arewa dai na dada bude ido bisa makoma ta kasar a karkashi na sabuwar gwagwarmayar kasar Yarabawan. A lokaci cikin tarihi dai yankin na Kudu maso Yamma na Shugaba Tinubun na zaman na kan gaba wajen neman sake fasali na kasar da kila damar ci na gashin kai.
Jefa a bangare na tsagerun Niger Delta wajen wani bikin yancin kai a karkashi na Jonathan dai ya diga dan bar bakin jini na gwamnatin har ya zuwa kare mata wa'adi.
Ita kanta gwamnatin kasar ta Buhari dai ta dandana hannunta a hannu na barayin dajin da mafi yawansu ke rayuwa a sashen na Arewa maso Yammacin kasar na Buharin. Kafin sabon yanayin yarabawan da ke zaman zakaran gwajin dafi ga gwamnatin Tinubun.
Barrister Buhari Yusuf dai na zaman wani lauyan da ke zaman kansa a nan a Abuja da kuma ya ce masu mulki na kasar suna bukatar bude ido da nufin tunkarar tsagerun na Ibadan da mafi yawansu suka sulale zuwa ga gonakin Goro da Kokon da ke a yankin na Kudu maso Yamma.
Koma ta ina Abujar ke shirin tabi cikin hanyar zare wandon karfen, wasu dai na kallon batun na wariya da idanu na siyasar kaiwa ya zuwa baki cikin kasar. Batun na wariya ne dai suka nuna wajen samun kaiwa ya zuwa dare mulki a bangaren NADECO ta 'yan kabilar Yarabawan shekaru 20 da doriya can baya.
Haka kuma neman sai ta waren ne yai nasarar samun dama ta kanana na kabilun yankin Niger Delta kaiwa ya zuwa mulki ddaga baya. To sai dai kuma wariyar a Zahiri na da illa ga makoma ta kasar a fadar Farfesa Kamilu Sani Fage da ke zaman kwararre a siyasa da kuma ya ce wasu sun gwada sun ci kasa.
Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba gashugaba Tinubun da ke tsakanin hukunta tsofaffi na abokan taku da suka hada da ita kanta Modupe Onitiri da ke zaman fuskar neman da a waren kuma tsohuwa ta mai dakin Chief MKO Abiola, jagora na siyasar Kudu maso Yamma kuma ubangida ga Tinubun a siyasa.