1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawo karshen tilasta zaman gida na IPOB

Muhammad Bello
September 13, 2023

Rundunar sojin Najeriya ta lashi takobin kawo karshen tilasta wa jama'a zaman gida da kungiyar rajin Biafra ta IPOB ke yi a yankin kudu maso gabashin kasar a duk ranakun litinin

https://p.dw.com/p/4WInt
Jami'in sojan Najeriya
Jami'in sojan NajeriyaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Manyan batutuwan baya-bayan nan game da ayyukan rundunar sojojin Najeriyar su ne na sake daura damarar tunkarar dimbin kalubalen tsaro da su ka dade su na addabar Najeriya, wadanda suka hada da Boko Haram da 'yan fashin daji da masu satar mutane a arewacin kasar. Rundunar sojin ta ce ta shirya tunkarar 'yan haramtacciyar kungiyar rajin Biafra IPOB da ke tilasta zaman gida ga jamaar yankin kudu maso gabashin Najeriyar tare da kassara harkokin yau da kullum.

Karin Bayani: 'Yan IPOB na kuntata wa jam'a a Ebonyi da Abia

Lt General Taoreed Lagbaja, shi ne babban hafsan sojojin Najeriyar.

Wasu yan kungiyar IPOB a Najeriya
Wasu yan kungiyar IPOB a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Ya ce a halin yanzu mun rubanya kokarin da mu ke yi wajen dakile takidin yan kungiyar rajin Biafra ta IPOB da dakarun kungiyar na ESN da ke aikata taannati a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Dakarunmu tare da hadin gwiwar bangarorin jamian tsaro, za mu kawo karshen wannan tilasta zaman gida da ke kassara harkokin yau da kullum a yankin.

Kakakin ungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Alex Ogbonnaya, ya baiyana farin ciki da wannan kudiri

Ya ce babban Hafsan sojin Najeriyar ya taba zama a rundunar soji ta 82 division da ke a Enugu, kuma ya san yankin kuma ina da kyakkyawar yakinin za a ci nasara.

Jami'an sojojin Najeriya
Jami'an sojojin NajeriyaHoto: AUDU ALI MARTE/AFP/Getty Images

To sai dai, wani dadadden zama a yankin na Igbo, na ganin cewar tunkarar kungiyar ta IPOB ba zai yiwu da karfin soja ba.

Cikin shekaru biyu na tsanantar ayyukan kungiyar ta IPOB musamman tilasta zaman gida ga jama'ar yankin, ya jawo hassarar rayukan jamian tsaro da fararen hula da dama, da kuma dimbin dukiya. Kimanin Naira Tiriliyan bakwai da biliyan 600 ne, yankin ya yi hassara sakamakon zaman gida da ke hana kowa kai kawo a yankin na Igbo.