1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar zaman gida a jihar Kano Najeriya

Nasir Salisu Zango LMJ
April 16, 2020

A Najeriya rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shirye domin tabbatar da dokar kowa ya zauna a gida domin dakile yaduwar annobar Coronavirus da ke karuwa a jihar.

https://p.dw.com/p/3b1z7
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

Zuwa yanzu dai mutane 21 ne aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan gano mutum na farko da aka fara ganowa ya kamu da cutar a jihar a ranar Asabar din da ta gabata. Kasuwanni dai cike suke da mutane da ke yin sayayyar karshe, kasancewar daga daren wannan Alhamis din dokar za ta fara aiki gadan-gadan a Kanon.

Tabbatar da ganin an bi dokar

Tun kafin cikar lokacin dai tawagar sojoji da 'yan sanda ke ta kewaye a cikin gari, domin nuna irin shirin da suka yi na dakile duk wata turjiya da ka iya kawowa doka kafar ungulu. DSP Abdullahi Haruna shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, ya ce sun gama shiri na tabbatar da cewa kowa ya zauna a gida domin ganin an yi biyayya ga wannan doka.To amma akwai unguwanni da dama a Kano wadanda ba su da ruwan sha, kuma sun dogara ne akan 'yan garuwa domin samun ruwa a kullum. Hakan ce ma ta sanya suke rokon mahukunta da a bari 'yan garuwa su gudanar da aiki, gudun samun wata matsalar.

Bombenexplosion Polizei in Nigeria
Jami'an tsaro za su tabbatar an bi dokaHoto: picture-alliance/AP Photo

Zuwa wuraren ibada

Wani abu da ka iya zama kiki-kaka ga wannan doka shi ne batun salla musamman ma ganin cewar gobe Jumma'a, to amma hadakar kungiyar malamai daga bangarori daban-daban, sun cimma matsaya kan cewar an dakatar da yin Sallar Jumma'a da karatuttukan tafsiri. Dr Muhammad Tahar Adamu Baba Impossible shi ne kwamishinan addinai na jihar Kano, ya ce malaman da kansu suka cimma wannan matsaya suka kuma fitar da fatawa.
Sai dai kuma ana yawan samun korafe korafe dangane da yadda cibiyoyin yaki da cutar na ma aikatar lafiya ta Kano ke tafiyar da aikinsu, inda sau da dama akan samu lakaki wajen zuwan su idan an shiga firgici. Haka kuma ba kasafai suke saurin kawo agajin gaggawa akan kari ba, zarge-zargen da ma'aikatar lafiya ke musantawa.

Coronavirus Bekämpfung in Afrika
Bukatar daukin jami'an kiwon lafiyaHoto: picture-alliance/dpa/O. Jaiyeola

Yanzu haka dai ana samun kungiyoyi da attajirai da ke dan rarraba kayan abinci ga mabukata, domin sanin cewar akwai dimbin mutane da a kullum sai sun fita za su samu abin kalace. A hannu guda wata majiya mai tushe ta bayyana cewar wani babban kusa a kwmaitin kar ta kwana me yaki da cutar ya kamu da Coronavirus din, har ma an killace shi a cibiyar killace masu cutar da ke kwanar dawaki. DW ta yi kokarin ji daga bakin mahukuntan ma'aikatar lafiya da kuma 'yan kwamitin, amma har hakanmu bai cimma ruwa ba. Mutane 21 ne dai aka tabbatar sun kamu da cutar a Kanon yayin da guda daga ciki ya rasu, sai dai har yanzu mutane sun shiga shakku kan hakikanin wanda ya rasun.