Karantsaye ga dokokin kariya a Najeriya
July 17, 2020Daya bayan daya dai hukumar kula da tashoshin jiragen saman Tarayyar Najeriyar ta FAAN ta rika kiran sunayen wasu manyan shugabanni na siyasa na kasar tana musu tofin Allah tsine, bisa abun da ta kira karan tsaye ga dokokin kare kai daga COVID-19 a bangaren sufurin sama da ya fara aiki cikin kasar daga makon jiya.
Rashin da'a daga manyan kasa
Kuma ya zuwa yanzun dai ta ambato gwamnan Adamawa Ahmed Umaru Fintiri da tsohon gwamna Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari da wani mamallakin kafafen yada labarai a kasar Nduka Ogbabeina a matsayin wasu a cikin marasa da'a da biyayya ga dokokin da gwamnatin kasar ke fatan ka iya kai wa ga dakile yaduwar cutar mai tasiri.
Kuma shi kansa ministan Sufurin sama na kasar Hadi Sirika ya ce an kaddamar da bincike da nufin hukunci cikin sabon laifin da ke barazana ga harkokin sufuri na sama a kasar. Ko bayan addini da bude kasuwa da nufin hada-hada ta rayuwa dai, bude tashoshin sufurin na sama na zaman babban fata ga 'yan kasar na sake sabuwar rayuwa a cikin annobar ta corona, kafin yunkurin da ke iya mai da hannun agogo zuwa baya a cikin neman hanyar dakile yaduwa ta cutar da ke ta karuwa a halin yanzu.
Zubar da kima da darajar kasa
Sababbi na matakan da suka hada da awo na zafi na jiki da kuma feshi na magani ga jakunkunan matafiya sannan da rage cunkuso a tashoshin dai, na zaman wasu a cikin ka'idojin zirga-zirga daga wani sashe zuwa wani cikin Najeriyar. Ka'idojin kuma da rushe su na iya kai wa ga rushe tagomashin kasar a idanun hukumomin duniya, a fadar Captain Bala Jibril da ke zaman wani masanin sufurin sama a kasar. Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a bangaren 'yan mulki na kasar, da ke neman hanyar kai karshen annobar a cikin hali na rashin da'ar manya d ake zaman abun koyin 'yan baya.