Najeriya, kisan malaman addinin Islama
November 5, 2014Cikin juyayi da zubar da hawaye ne saboda takaicin abinda ya faru ne aka sallaci shehin malamin a gidan sa da ke garin Nafada da sauran daliban sa da aka hallaka kamar dai yadda addinin musulunci ya tanadar. Daruruwa dalibai da masoya da ‘yan uwa da abokan arziki ne suka halarci wannan jana'iza ta sheikh Adamu Muhammad Nafada daya daga cikin malaman Hadisi na duniya da jami'an kasar Misra wacce aka fi sani da jami'atul Azhar ke tinkaho da su.
Tarihin Adamu Muhammad Nafada
An haifi sheihk Adamu Muhammad a garin Nafada a shekarar 1937 inda ya yi daukacin karatun sa a kasar Masar a gaban sanannen malamin addinin Musuluncin nan na kasar Sheikh Hafiz Al-Misry. Ya kuma yi wasu karance-karance a jami'oi da kuma gaban wasu malamai a kasashen Siriya da Maroko kafin dawowar sa gida bisa umurnin malaminsa don karantar da al'umma da kuma yada addinin Islama. Ko wanene Sheikh Adamu Muhammad Nafada wanda aka fi sani da Sheikh Adamu Misra tambayar da na yiwa daya daga cikin daliban sa kenan wanda ya bani amsa bisa sharadin zan sakaye sunan sa saboda dalilan na tsaro.
Waye Sheikh Adamu Nafada?
Tsawon rayuwarsa sama da shekaru 40 da yayi a garin Nafada bayan dawowar sa da ga karatu Sheikh Adamu Nafada ya kasance mai koyar da karatun Al-Qur'ani da kuma litattafai inda daruruwan almajirai suka zama malamai a hannunsa ciki kuwa har da ‘ya‘yan sa. Da yawa daga cikin wadan da suka san wannan shehin Malamin sun bayyana alhininsu na wannan rashi, da suka yi imanin cewa zai haifar da gagarumin gibi mai wuyar cikewa. Sheikh Adamu Muhammad Nafada ya samu shaida ta yin zaman lafiya da kowa har ma da wanda ba Musulmi ba abinda yasa mabiya addinin kirista ma suka nuna nasu juyayin. Kisan malaman addinin Islama dai ba bakon abu bane a kasar.