Najeriya ta sake salon magance matsalar manoma da makiyaya
February 5, 2020
Kwarraru a cikin harkokin noma dana kiwo ne suka sun share tsawon yini guda suna nazarin matsalar da ta mamaye daukaci na sassan tarrayar Najeriya da ke neman ta gagari kundila. An turance dai an kallo sauyin yanayi da gwagwarmaya da yin tasiri a bangare guda biyun a matsayin ummul'abaisin annoba da ke zaman kan gaba cikin rigingimun kasar.
Asalin matsalar dai ta faro tare da mamaye burtalolin kiwo a bangare na manoma sannan kuma ta abkawa gonaki ga masu sana'ar kiwon. Rikicin ne dai har ila yau ake yi wa kallon ummul'aba'isi na garkuwa da mutane bayan kare shanun da akai nasarar sacewa a bangare na matasa na Fulanin.
Ya zuwa yanzu dai daukacin jihohin arewacin Najeriya sun amince da wani shirin a sake tsugunar da masu sana'ar kiwon a cikin neman rage cudanyar da ake yi wa kallon ummul'aba'isin rikicin mai hatsari. Najeriyar na tsakanin mai da sana'ar noma a gaban kowace ta zamani amma a cikin rikici na rashin yarda da amincin al'umma daban daban.