Najeriya: Kokarin yin sulhu da majalisar dattawa
March 29, 2017Sannu a hankali dai rikicin na kara tsamari, sannu a hankali kuma yana barazanar tsaida daukacin harkokin mulkin Tarrayar Najeriya inda a halin yanzu ake kara jan daga a tsakanin bangaren zartarwa da kuma na majalisar.
Babban batu dai na zaman na raini da rashin mutuncin da 'yan dokar ke zargin wasu jami'ai na gwamnatin kasar da yi musu, abin kuma da ya harzuka 'yan majalisar ya zuwa daukar jeri na matakai.
Ko bayan dakatar da aikin tantance wasu jerin sunaye 27 da shugaban kasar ya aika domin zama kwamishinonin zabe na kasar dai, majalisar dattawan ta kuma dage aikin kasafin kudin kasar har ya zuwa watan jibi na Mayu tare da sharadin tsige shugaban hukumar yaki da cin hancin kasar ta EFCC.
Akwai kuma tsoron yiwuwar mantawa da su kansu sababbin ministoci guda biyun da suka hada da Sulaiman Hassan daga Gombe da Stephen Ocheni daga Kogi.
Matakin sulhu cikin gaggawa
Sabon rikicin dai ya dauke hankalin majalisar zartarwa ta kasar da ta share zamanta da yammacin ranar Larabar nan ta kuma aiyanna wani kwamiti a karkashi na mataimaki na shugaban kasar domin sulhunta tsakani.
Alhaji Lai Muhammad dai na zaman ministan labarai na kasar kuma kakaki na gwamnatin ta Abuja, da kuma ya ce ai rikicin ba sabo ba ne ga kowane yanayi na demokaradiyya ta kasar.
"A kowace demokaradiyya batu ne na gwagwarmaya, kokarin daidaito a tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa, kuma wannan batu ya ja hankali na majalisar zartarwa kuma an kafa kwamiti da nufin warware batutuwan."
To sai dai kuma ko mai nisan tattaunawar da majiyoyin fadar gwamnatin suka ce za ta dau fasalin ganawa ta kai tsaye a tsakanin 'yan zartarwar da abokan takun nasu na doka dai, daga dukkan alamu zabi na tsakanin tsige wasu a cikin jami'ai na gwamnatin kasar da kuma barazanar tsaida daukacin harkokin mulki.
Barazanar kuma da ke kara nuna alamun tasiri tare da dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar Senata Ali Ndume da ya yi nisa a wajen goyon bayan fadar ta Abuja.
Ana dai kallon rikicin na zama alamu na irin fasalin da kasar ke shirin dauka a gaba, cikin fagen siyasa, inda yanzu haka bangarori ke jan daga sannan kuma kowa ke neman inuwar rabewa domin taka rawa a gaba a cikin jam'iyyar APC mai mulki.