Najeriya: Korar zaunannun likitocin manyan asibitoci
June 22, 2016Duk da cewar dai sun dauki lokaci suna jani in jaka a bisa jeri na bukatu da gwamnatin, wata sanarwar ma'aikatar lafiya ta Najeriya dai ta zo a ba zata ga zaunannun likitocin kasar da ke neman kyautata albashi da tsarin aiki amma kuma suka kare da rasa aiki gaba daya.
Sanarwar da ke dauke da sa hannun kakaki ta ma'aikatar ta lafiya dai ta ce ministan lafiyar kasar ya umarci manyan daraktocin asibitoci na gwamnatin tarayya da su mika takarda ta sallama tare da fara daukar aikin wasu likitoci nan take.
Matakin na gwamnati dai ya biyo bayan rushewar tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu bisa karin albashi da kyautata yanayin aiki. Sama da likitoci dubu 16 ne dai sabon matakin yake shirin shafa karkashin tsarin da ke kallon kananan likitoci kara samun kwarewa da zama manya da taimako na gwamnatin.
Goyon bayan matakin gwamnati
To sai dai kuma tuni matakin ya fara jawo martani a bangare na 'yan kasar da suka dauki tsawon lokaci suna ji a jiki sakamakon yajin da ya gurgunta daukacin manyan asibitocin koyarwa na kasar. Ga dai ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya.
"Son rai ne ya yi wa likitoci yawa, amma ba wai suna da gaskiya ba ne. Sallar tasu ita ta fi dacewa, sai dai matsalar guda daya ce wato shin gwamnati tanan da isassun kilitoci kuma kwararru da za su maye gurbin wadanda za ta korar?"
"Gaskiya matakin da gwamnati ta dauka ta yi daidai, domin likitocin ba su yi wa kansu adalci ba ba su yi wa 'yan Najeriya adalci ba. Ai ba su kadai ne ma'aikata a Najeriya ba. Me ya sa su kowace shekara sai sun shiga yajin aiki."
Kokarin shiga tsakani don samun mafita
To sai dai koma tana ina likitocin ke iya fuskantar korar tasu dai kokarin ji daga bakinsu ya ci tura bayan da wani a cikin shugabanni na kasa ya ce ba su da niyyar maida martani har sai bayan kammala wani taronsu a ranar Alhamis.
Shekarun baya-baya dai tsohuwar gwamnatin da ta shude ta sallami zaunannun likitocin kafin daga baya a zauna a sake sassantawa tare da mai dasu zuwa bakin aiki.
Tuni dai likitocin suka amince su koma bakin aiki akalla har ya zuwa tsakiyar watan gobe duk da sallamar tasu a bangaren mahukunta na kasar.
To sai dai kuma har ya zuwa yanzu ma'aikatar lafiyar ba ta aiyyana ko ta janye sallamar da ke iya karin dagula lamura a cikin masana'antar lafiyar kasar da ke fuskantar karancin ma'aikata ba.
Yanzu haka dai shugaban majalisar wakilin kasar Yakubu Dogara ya amince ya shiga tsakanin bangarorin biyu da nufin samun mafitar rikicin mai hatsari.