1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta saki wasu 'yan Shi'a

Gazali Abdou Tasawa
November 9, 2017

A Najeriya babbar kotun Kaduna ta saki wasu mabiyar mazahabin Shi'a goma daga cikin daruruwan da aka kama tare da jagoransu Cheik Ibrahim Zakzaky shekaru biyu da suka gabata biyo bayan wata arangama da sojoji a Zaria

https://p.dw.com/p/2nNda
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

A Najeriya babbar kotun Kaduna ta saki a wannan Alhamis wasu mabiyar mazahabin Shi'a su goma daga cikin daruruwan 'yan Shi'ar da aka kama tare da jagoransu Cheik Ibrahim Zakzaky shekaru biyu da suka gabata biyo bayan wata arangama da suka yi da sojoji a watan Desambar 2015 a garin Zaria inda 'yan Shi'a sama da 300 suka halaka a cewar alkalumma hukuma. 

Alkalin babbar kotun ta Kaduna Esther Lolo ta ce ta saki mutanen ne bayan da wadanda suka shigar da kara kansu suka kasa kawo gamsassun hujjoji  da ke nuni da cewa wadannan mutane 10 sun aikata laifin da ake zarginsu da aikata da suka hada da shirya wa kasa makarkashiya, aikata ta'addanci, tayar da tarzoma, halartar wani taron gangamin da hakuma ta haramta. 

Sai dai kotun ba ta ce komi ba ya zuwa yanzu a game da makomar sauran daruruwan 'yan Shi'ar da ake tsare da su. Dabra da wannan umurni na kotun ta Kaduna, lauyan Cheikh Zakzaky ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ba da umurnin a saki shehin malamin da mai dakinsa a bisa dalillai na rashin lafiya.