1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotun sauraren kararrakin zabe ta fara zama

Uwais Abubakar Idris
May 8, 2023

An fara sauraron shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa a Abuja inda jamiyyu biyar ke kalubalantar nasarar zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu

https://p.dw.com/p/4R3yL
Bildkombo Nigeria Wahlen | Peter Obi, Bola Tinubu (M), Atiku Abubakar
Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

Wakilan jamiyyun da ke kalubalantar hukumar zaben Najeriyar INEC da zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu sun hallara a kotun wacce mai shari'a Haruna Simon Tsammani ke jagoranta tare da sauran alkali hudu da ke taimaka masa. Ya yi alkawarin za su yi wa kowa adalaci a shari'ar da yake son hatta alummar Najeriya su hallarci zaman don zama shaida.

Tun da farkon shari'ar ne dai jamiyyar Action Alliance wacce dan takararta Major Hamza Almustapha mai ritaya ya tsaya mata takara ta sanar da janye kararsu tare da bayyana goyon bayansu ga zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu. Barrister Dauda Abdulmalik Usman shi ne lauyan da ke kare jamiyyar ta Action Alliance.

An dai ci gaba da sauraron bahasi na dalilan kararar da sauran jamiyyun suka gabatar inda aka fara da jamiyyar Labour wadda dan takararta na neman shugaban kasa Peter Obi ya bayyana a kotu, lauyoyin sun yi bayani dalilan da suka sanya su zuwa kotu. Dr Yunusa Tanko na cikin wadanda suka saurari zaman kotun.

Akwai dai jamiyyun All Peoples Party da na All Peoples movement da dukkaninsu aka saurari bahasinsu a kotu. Barrister Livi Uzorkwu ya bayyana tasirin shari'ar da suke fatan ganin an yi.

"Ya ce sakamakon shari'ar da za'a bayar zai yi tasiri ga shari'oin zabe da ma tsarin mulkin Najeriya, domin ta kowace hanya bana jin a wannan karon kamar yadda aka saba ne. Mun bai wa kotu tabbacin cewa za mu yi duk abinda muka iya mu tabbatar da an hanzarta wannan sharia' domin kowa ya sa ido yana jira".

Za'a ci gaba da sauraren shari'ar inda jamiyyar PDP za ta gabatar da nata bahasin. Mai shari'a Harun Simon Tsammani ya bukaci lauyoyi su kauce wa jawo abinda zai sanya jinkiri a shariar. Alamu na nuna ba za'a iya samun hanzarin yanke hukunci a shari'oin zaben shugaban Najeriyar ba, duk da cewa sauran makwanni uku a rantsar da Bola Ahmed Tinu a wannan mukami.