1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kubutar da fasinjojin jirgin kasa daga hannun 'yan bindiga

Binta Aliyu Zurmi
August 12, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kubutar da sauran fasinjojin jirgin kasa mutum 31 da ake ci gaba da garkuwa da su watanni biyar bayan sace su da 'yan bindiga suka yi.

https://p.dw.com/p/4FRbn
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Wannan jawabi na shugaban na zuwa ne bayan wata ganawa da ya yi da 'yan uwan fasinjojin a Abuja, ya kuma tabbatar musu da gwamnatin sa na yin iya kokarinta na maido da yan uwansu gida cikin koshin lafiya.

Sai dai tun a farkon makon da aka kwashe mutanen gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen kubutar da wadannan mutanen, rashin katabus da 'yan uwan fasinjojin ke zargin gwamnatin ya kai su ga biyan makudan kudade domin kubutar da 'yan uwansu.

Ko a wannan makon ma an sako wata mata da ke da kanana yara hudu daga daji, sai dai babu tabbacin ko sun biyu kudin fansa.

Najeriyar dai ta shafe shekaru tana fama da ayyukan ta'addanci, wanda biyan kudin fansa domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su ke neman share wuri ya zauna a kasar da ke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka wanda kuma ke fama da mastin rayuwa.