Matakan inganta wutar lantarki a Najeriya
March 12, 2020Ci gaba da tabarbarewar harkar samar da wutan lantarki a Najeriya duk da makuddan kudaden da ake zubawa wannan sashi da ya kai ga cefanar da wasu sassansu a hannun ‘yan kasuwa, ya sanya gabatar da wannan kuduri. Dokar da suke hasashen zata taimaka bunkasa harkar wutar lantarki a Najeriyar Sanata.
To sai dai tuni lamarin ya sanya maida martani daga ‘yan Najeriya da dama, sanin cewa an fi dogaro a kan Janaraito fiye da kamfanin wutar lantarki na kasar duk da mayar da shi hannun ‘yan kasuwa.
Ta dai ta kaiga hatta majalisar dokokin Najeriya na kasafta makuddan kudade wajen shigo da Janaraito a kasar, amma ga Injinya Ahmed Zakari Nguroje wanda kwararre ne a wannan fanin ya ce a hasashensa akwai amfani ga wannan.
Ta dai kaiga gwamnatin kurarin na amshe harkar wutar lantarkin daga kamfanonin kasar saboda gazawarsu da ma zargi na makarkashiya, domin daga cikin megawatt dubu 13 da ake samarwa dubu uku ne suke iya saye su rarrabawa ‘yan Najeriya abinda ke haifar da zargi na makarkashiya.