Najeriya: Kunci a Legas kan dokar haramta Adaidaita Sahu
February 4, 2020A dangane da halin rayuwa a Lagos da ke Najeriya, musamman ta sufuri ko shakka babu mazauna birnin na ji a jikinsu. Batu na 'Yan Acaba ko Adaidaita Sahu a birnin na neman zama tarihi, tare da barin jama'a na yin gararamba a kan tituna walau manya ko kanana da neman ababan hawa don zuwa wajen aiki .
Bincike ya tabbatar da cewa a yanzu har da masu kekuna sun fito suna kwasar ganima inda wani mai suna Bulasma ya ke cewa shi ya gano hanyar samun kudi tunda an hana Okada.
''Daman yayana yana da keke, saboda haka na fito da shi, sai na lura cewa mutane na bukatarsa saboda sun gaji da tafiya, ni kuma na mika kai kawai, a kan haka a kalla na sami kusan naira dubu biyu, tun daga ranar Asabar kawo yanzu, abin da na ke yi kenan ni yanzu, kuma Alhamdulillah''
Bugu da kari direbobin manyan motoci masu nunfashi kan saci hanya daga iyayen gidansu don samun kudin kalace kamar yadda malam ya shaida wa wakilin DW a Lagos din inda yake cewa:
''Duk wata mota ta alfarma zaka same ta a yankin Folomo ko Golden Gate, ko Pand T, don daukar fasinjoji zuwa wurare kamar su Oshodi, ko Ikeja, kuma cikin farashi mai sauki''.
Jama'a dai kowa sai kokawa ya ke, banda wadanda suka rufa suka tayar da kai, Malam Usman Abike Ade, ga abin da ya ke cewa shi ma:
''Batu na gaskiya mutane naji a jikinsu, sabili da sabbin matakan da gwamnati ta dauka na haramta anfani da Okada da keken marwa ko kadan bai dace ba''.
Mr Abiodun ya riski wakilin DW a fusace, inda ya ke cewa a fada wa shugabanni halin da suke ciki, yana mai cewa:
''Haramta Okada da aka yi ba laifi, amma hana Keken Marwa bai dace ba, yanzu ina zaune a Saleko na zo cMc ba keke, na zo Obalende ba Keken Marwa nan ma, sai da na tako da kafa, wannan kuwa babban kalubale ne ga duk mazauna Lagos''.
To sai dai, daya daga cikin shugabannin kungiyar Okada da Keken Marwa ta kasa, Dr Muhd Musa mai takobi ya ce hakuri shi ne magani, inda ya kara da cewa:
''Ina shawartar 'yan uwa da su rungumi matakin zaman lafiya da hukuma tun da dai ta ce ba ta bukata, saboda haka sai muyi hakuri''
A yanzu haka dai gwamnatin Lagos ta tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya kan wannan batu, sai dai ta yi alkawarin kawo sabbin motoci 550, a nan gaba kadan, kuma ta amince da bayar da sabbin motoci na BRT 65, ga wurare daban-daban na birnin Lagos.