Najeriya: Kungiyar malamai ASUU ta janye yajin aiki
October 14, 2022Mambobin majalisar zartaswar ta kungiyar malaman jamioi’n Najeriyar sun kwashe daukacin daren juma’a suna tattaunawa inda a karshe suka cimma matsayar janye yajin aikin da suka kwashe watanni 8 suna yi,
Yajin aikin dai ya gurgunta harkokin karatu a jamio’in kasar baki daya. Dr Chris Piwuna mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar da janye yajin aiki.
Ko da yake sun danganta janye yajin aikin a kan bin umarnin kotu, amma bayanai sun tabbatar da cewar shiga tsakanin da shugaban majalisar wakilan Najeriyar Hon Femi Gbajabiamila ya yi ya sanya gwamnatin ta sassauto inda ta amince za ta biya malaman albashin watani hudu sannan za’a rarraba na sauran watanin, kuma an sanya batun yi masu karin albashi da kudadden farfado da jamio’i da suke korafi a kai a kasasfin kudi.
Tuni iyayen yara suka fara murna a kan wannan ci gaba.
Yanzu za’a jira shugabanin jami’oin su sanar da ranar da za’a koma a ci gaba da karatu.