Najeriya: Lalata bututun mai a yankin Niger Delta
November 16, 2016Talla
Sanarwar da 'yan kungiyar na yakin Niger Delta suka wallafa a daren Talata wayewar Laraba, ta ce da misalin karfe 11 da mintuna 45 ne wasu mayakansu su 15 suka aiwatar da aikin fasa bututun mai na kanfanonin AGIP da Oando da kuma Shell, wandanda ke iya shigar da gangan danyan mai 300.000 a rana ya zuwa babbar cibiyar fitar da man ta Bonny da ke jihar Bayalsa.
Sai dai babu wani martani da ke tabbatar da hakan daga hukumomin na Najeriya, ko kuma kanfanonin da wannan sabon ta'annati ya shafa. Batun ta'annatci kan bututun man na Najeriya dai, ya sanya kasar Angola shiga gaba a matsayin wadda ta fi ko wacce kasa arzikin mai a Afirka.